Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burina Arewa Ta Shiga Taswirar Duniya A Fagen Waka: Haruna Abdullahi


Haruna Abdullahi
Haruna Abdullahi

Wani matashin mawaki Haruna Abdullahi, wanda ake kuma kira DJ AB, yace babban burinsa shine ganin arewa ta shiga tasawirar duniya a dama da ita a faggen nishadantarwa.

Ya kara da cerwa an bar arewa a baya a fannoni da dama, ya ce harkar waka harka ce mai kawo kudi sannan hanya ce ta fadakarwa da wa’azantar kamar yadda ake isar da sako ta hanyar karatu sannan hanya ce da za’a inganta tare da tallata harshen Hausa.

DJ AB , Furodusan waka, mawakin hip-hop da kuma dance hall waka da rawa a lokaci guda, ya ce yana isar da sakonin ta hanyar bada labarai masu fadakarwa da nishadi mussamam sakonnin irin soyayyar da ake yi a zamani na dan lokaci da kuma ire-iren tufafin da matasa ke sawa a yanzu.

Ya ce baya fuskantar kalubale kamar ragowar mawakan hip hop a cewarsa domin baya nuna mata da rawar da bata dace ba ko shan sigari da wasu abubuwan da basu dace ba.

DJ AB ya ce a yanzu haka yana jami’a kuma karatun da yake yi bai hanashi cigaba da wakarsa ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG