Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kubutar Da 'Yar Shekaru 13


BORNO: Yan gudun hijira
BORNO: Yan gudun hijira

Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta kubutar da wata yarinya mai shekaru goma sha uku,Nkechi Oseh daga gidan wata mata mai suna Betty Ifeoma wadda ta tsare ta a gidanta na tsawon makwanni tana aikatau.

Mai rikon Kwamishinan ‘yan Sandan, jihar Legas, Imohimi Edgal​ne ne ya jagoranci kubutar da yarinyar a gida mai lamba 30, a layin Adeniran dake rukunin gidajen unguwar Ajao.

An yi sa'ar kubutar da yarinyar bayan da hukumar ‘yan Sanda ta samu tsegumin cewa a duk lokacin da Betty za tayi tafiya sai ta kulle yarinyar na tsawon lokacin da zata yi kuma babu abinda ta ke bar mata na ci face kwalin biskit na cabin guda biyu.

Nkechi, wacce take mareniya ce ta sha azaba iri-iri a hannun Betty. A yanzu dai ta koma karkashin kulawar hukumomin jihar Legas.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG