Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baba Jada Yayi Kira Ga ‘Yan Wasan Wikki Tourist Su Zage Damtse


Baba Jada, Wikki Tourist
Baba Jada, Wikki Tourist

A ranar Litinin 15/5/2017 Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagoranci mai girma Gwamnan jihar Bauchi, Brr Mohammed Abdullahi Abubakar, ya amince da nada sabon kwamiti don ceto kungiyar kwallon kafa mallakar jihar Bauchi Wikki tourist.

Domin halin da ta tsinci kanta a ciki, kungiyar ta Wikki, tourist ta kasa tabuka abun azo a gani a bana inda aka shiga tsakiyar kakar wasa ta NPFL 2016/17, kungiyar tana matsayi na goma sha tara a kasan teburin Firimiyar Najeriya, da maki ashirin da daya kacal, Sa banin shekarun baya da suka wuce wanda Wikki, ta kammala a matsayi na ukku har ma ta wakilci tarayya Najeriya, a gasar CAF.

A satin da ya gabata, gwamnatin jihar ta bada sanarwar sauke hukumar gudanarwa ta kungiyar, karkashin jagorancin Hon Isa Musa Matori.

A yanzu kuma ta nada kwamiti mai mutane 7 da zasu farfado da Kungiyar, karkashin jagoranci shugaban ta Alhaji Auwal Baba Jada,

Sakatare Abdullahi Ibrahim Askiya, Mai bada shawara Pascal Patrick (Mon), Sai mambobinta Mohammed Bawa ATBU, akwai Sadiq Yusuf Baba, Umar Ahmed Ilelah, da kuma Paul Gambar, wanda aikinsu ya fara nan take.

Bayan kama aikinsu ke da wuya shugaban kungiyar Baba Jada, ya ja hankalin ‘yan wasan da su kara damara don ganin kungiyar ta samu nasarar ficewa daga cikin halin da take ciki a hirar da sukayi da wakilin dandalinvoa, Baba Jada ya kara dacewa yana bukatar hadin kan abokan aikinsa da kuma Kungiyar magoya bayan Wikki tourist, da jama'ar gari don samun nasara akan wannan Jan aiki da yake gabansu.

Daga bisani sunkai wa kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar Pharmacy Ibrahim Madaki Saleh, ziyara da kuma fadar mai martaba Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulemanu Adamu, domin neman tabaraki

ga abnda Baba Jada, yace cikin hirar da akayi dashi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG