Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atletico Madrid Zata Kara Da Real Madrid


A cigaba da fafatawa da akeyi a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai UEFA Champions league 2016/17 a matakin wasan kusa da na karshe (semi final) jiya kungiyar kwallon kafa ta Juventus, ta samu nasarar zuwa wasan karshe na UCL, na bana bayan ta doke takwararta ta Monaco daci 2-1 a karawarsu ta biyu inda a haduwarsu ta farko Juventus tabi Monaco, har gida ta shata 2-0 wannan yasa Juventus, take da jimillar kwallaye, 4 ita kuma Monaco 1.

Shekaru ashirin da daya kenan rabon Juventus, ta dauki wannan kofin tun shekarar 1996, inda a yanzu haka take jiran daya daga cikin Atletico Madrid ko Real Madrid, domin buga wasan karshe na bana.

A yau Atletico Madrid, zata kara da Real Madrid, a gasar ta Uefa Champions league 2016/17 semi final Zagaye na biyu a satin daya gabatane Real Madrid, ta lallasa Atletico Madrid, a karawarsu ta farko da kwallaye 3-0
yanzu haka Atletico Madrid, na neman kwallaye 4 da babu kafin ta kai ga wasan karshe a UCL na bana.

Ita kuwa Real Madrid, na bukatar kunnen doki ko yaya don ta samu damar hayewa zuwa wasan karshe. Za'ayi wannan wasanne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG