Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ke Kan Gaba A Lashe Firimiya Lig


Paul Pogba na Manchester United
Paul Pogba na Manchester United
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu nasarar lashe gasar Firimiya lig na bana na kasar Ingila.
Chelsea tayi wannan nasaran ne ranar Jumma'a da ta gabata bayan da ta doke Westbromwich da ci daya mai ban haushi a gasar ta Firimiya mako na 37.
Inda a yanzu haka take da maki 87, a mataki na daya Tottenham, tana mataki na biyu da maki 80, sai Liverpool ke biye da ita da maki 73, Manchester City tana mataki na hudu da maki 72, inda ita kuma Arsenal ke matsayi na biyar da maki 69.
Wannan shine karo na biyar da kungiyar ta Chelsea ke lashe gasar a tun bayan da aka Chanja wa gasar suna zuwa Firimiya.
Chelsea itace kungiya ta biyu da tafi kowa daukan wannan kofin
Manchester United ita take kan gaba wajan lashe Firimiya lig na kasar Ingila inda ta dauki kofin sau 13, Arsenal sau 3, sai Manchester City sau 2,
Blackburn sau 1, Leicester City sau 1.
A yanzu haka dai saura wasa daya na mako 38 ya rage a kammala wasan na bana sai dai akwai wasu kungiyoyin da suke da wasu kwantan wasa da basuyiba.
A yau kungiyar Chelsea zata kara da Watford a kwantan wasa da basu bugaba na mako na ashirin da takwas Za'ayi wasan da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:44 0:00

XS
SM
MD
LG