Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amir Khan Zai Dambata Da Manny Pacquiao A Saudi Arebiya


Matashin dan wasan danben kasar Burtaniya, Amir Khan da aka haifa a garin Bolton, ya gudanar da taro manema labarai a yau Talata a farfajiyar wajen motsa jiki a garin Bolton.

Khan yace ya rattaba hannu don danbatawa a ranar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa a Riyadh babban birnin kasar Saudi Arebiya, haka abokin karawarsa Manny Paquiao ya rattaba hannu akan yarjejeniyar shima.

Sai dai dan danben na kasar Burtaniya an biya shi fan miliyan bakwai bayan da yayi galaba akan Billy Dib a makon da ya gabata, da shima aka danbata a Saudi Arebiyar.

Manny Pacquiao dan shekaru 40 da haihuwa yanzu, zai fafata a wasan kwararru da ya dambata na 71 a karshen wannan satin, a gasar ajin masu nauyi da ake kira (WBA) “Super” tare Keith Thurman.

Pacquiao shine har yanzu yake rike da daya kambun na (WBA).

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG