Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbatar Yanayi Na Haddasa Mutuwa A Fadin Duniya


Gurbatar yanayi na haddasa matsaloli da dama, ana iya cewa yaro daya cikin hudu ke mutuwa ‘yan kasa da shekaru 5, a fadin duniya, wanda adadin su ya kai milliyan daya da dubu dari bakwai.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta tabbatar da cewar idan har ba’a dauki kwararan matakai ba mutuwar zata karu matuka, idan har ba’a dauki matakan kawo karshen gurbatar yanayi ba.

Hukumar ta kwatanta matsalolin da gurbatar yanayi ke haifarwa ga yara, da fitar da hanyoyi biyu don magance hankan, a wani bincike da suka gudanar, masu take “Riko da yanayi mai dorewa a duniya” da “Maida hankali ga lafiyar yara da yanayi.”

Burin shine kada a gurbata yanayi, don kariya ga yara da yanayin da jama’a ke rayuwa, don samun lafiya mai inganci. A cewar masana, gurbattacciyar iska da jarirai ke shaka na zama sanadiyyar mutuwar yara sama da milliyan 6.5 a kowace shekara.

Wannan ya hada da yara sama da 600,000 masu shekaru daga daya zuwa biyar na haihuwar su. Margaret Chan, darakta janaral ta hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta bayyana cewar kananan yara suna cikin hatsari na mutuwa a lokacin da suke da kanana shekaru.

Kuma mafi akasarin yaran dake mutuwa sun fito daga kasashe masu tasowa ne, wanda gurbatacciyar iska da ake shaka ke da alaka da kasashe masu arziki da masu fama da talauci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG