Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Sakon Badda Kama, Dauke Da Macizai 3 Daga Hong Kong


Sakon Macizai
Sakon Macizai

Jami’an shige da fice na kasar Amurka ‘Customs’ sunyi arangama da wani matashi Mr. Rodrigo Franco, mai shekaru 34, a jihar California ta kasar Amurka. Biyo bayan wani sako da aka aikoma matashin daga kasar Hong Kong.

Sakon da aka aiko mishi a cikin wani karamin gwangwani na dauke da kananan macizai ‘Cobra’ guda uku, dayan gwangwanin kuwa na dauke da ‘ya’yan Kunkuru. Bisa dokokin kasar Amurka, killace wadannan dabbobin haramun ne ga dokar kare hakkin dabbobi.

A dai-dai lokacin da suka lura da sakon na dauke da wani abu, sun bude don tabbatar da abun dake ciki, daga baya sun aika mishi da jariran kunkuru gidan shi, amma suka rike macizan, don gudun cutarwa ga wani.

Daga baya jami’an bincike sun ziyarci gidan shi, don ganin irin abubuwa da yakeyi da irin wadannan dabbobin, koda suka shiga cikin wani daki, sunga wata jarka dauke da jariran kada, dankareren kada, jariran kunkuru.

A cikin binciken su, sunga inda ya aika da sakon gaggawa ga wani dan’uwan shi, inda yake tabbatar mishi da cewar ya taba karbar sakon kaya irin wadannan, don wanncan ya aiko mishi da sakon, da alkawalin cewar zai bashi guda biyar daga cikin macizan.

Ya bayyanama kotu cewar a baya, ya karbi sakon dabbobi irin wadannan daga kasashe daban-daban. Yanzu haka dai yana tsare don amsa tambayoyi, idan kuma aka kamashi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin gidan kasu na tsawon shekaru 20.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG