Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taswirar Zanen Hannun Mutun Na Bada Kariya Wajen Satar Waya


Wani cigaba kan iya zama mafita ga rayuwar yau da kullun. Musamman idan akayi la’akari da yadda cigaban zamani yake kara bama mutane dama, wajen amfani da zanen hannu don kulle waya ko kwanfuta, a matakin kara samar da tsaro.

Sau da dama mutane kanyi amfani da yatsan su, wajen kulle waya, ba sai sunyi amfani da lambobi da akanyi amfani da su wajen kulle wayoyin hannu ba. A wasu lokkuta hakan yakan iya zama mafita, a wasu lokkuta kuma su kan iya zama matsala ga sirrin mutane.

A yunkurin su na magance matsalar amfani da lambobin sirri, kamfanin Apple, Microsoft, da wasu kamfanonin kimmiya, na shawartar mutane da su kokarta, wajen amfani da zanen hannun su, wajen kulle wayoyin su da kwamfutoci, don kara karfin tsaro mai inganci. Suna kara kaimi wajen samar da wata kafar amfani da kwayar ido don bude waya, a cikin yunkurin samar da tsaro mai nagarta.

Wayoyin zamani a nan gaba, zasu fara zuwa dauke da wasu manhajojin zamani, da zasu dinga taimakawa wajen amfani da jikin mutun don bude waya, hakan zai taimaka wajen rage satar waya, don bazata yi amfani da alamun jikin wani ba, idan bana ainihin mai wayar ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG