Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Na Gabda Fitar Da Sabuwar Wayar iPhone 8


Sabuwar Wayar iPhone 8
Sabuwar Wayar iPhone 8

Kwanaki kadan da suka rage, kamfanin Apple su fitar da sabuwar wayar su ta iPhone 8, kusan ana iya cewar jama’a sun kusan gama sanin sabon tsarin dake cikin wayar. Kamfanin dai na kokarin cika shekara 10 da kafuwa.

Ana sa tsanmanin zasu fitar da wata sabuwar kala mai ruwan madubi, ana kuma sa tsanmanin za’a fara siyar da abubuwan cajin wayar kamar su cajar tafida gidanka, cajar mota, da zarar an saka ranar da za’a fitar da wayar a kasuwa.

Wayar dai da ake hasashen zatazo a kaloli kamar su Jet Black, Black, Silver, Gold, Rose Gold da Red. A baya dai mutane da dama sun nuna fifikon su a wajen wace kala sukafi sha’awa, don haka wannan karon anasa ran kamfanin zasu yawaita kalar ja cikin wayoyin.

Ana kuma tsanmanin kamfanin zasu sadaukar da wayar mai kalan toka, ganin cewar suna bukin cika shekaru 10, hakan kuma yasa suka fito da sabuwar kala mai kalan madubi, wanda bata kurzunewa ko kadan.

Kana anasa ran sabuwar wayar zata zo da dama da mutun zai bada wani abu na son ra’ayin shi a saka mishi acikin wayar, kamar yadda ake da damar mutun yayi amfani da zanen yatsan shi wajen budewayar ko amfani da fuskar mutun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG