Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakuna 4 Daga Gidan Zoo Din 'Kruger' Sun Ranta A Na Kare


Zakuna
Zakuna

Dubun dubatar malaman gandun daji ne suka bazama, cikin kungurmin dajin kasar Afrika ta kudu, don neman wasu Zakuna guda hudu da suka kubce daga gidan Zoo. Zakunan dai maza ne, sun gudu daga gidan kallo na ‘Kruger National Park’

A tsakar daren Lahadi da ta gabata ne suka samu nasarar tserewa, akaron karshe da aka gansu a wani karamin gari mai suna Matsulu, a cewar mahukunta gidan zoo din, cikin wani bayani da suka fitar.

Kewaye da kauyen na Kruger, akwai alkaryoyin jama’a da gonakin su, kana da dabbobin su. Wannan wani babban kalubale ne ga rayuwar al’umar yankin da dukiyoyin su. A watan Mayu da ya gabata wasu zakuna 5 sun taba guduwa, amma ansamu nasarar kamo su.

A shekarar 2015, wani Zaki mai suna Sylvester, wanda ya silale ta karkashin waya mai wuta, daga wani gidan zoo, ya fita inda ya kwashe tsawon sati 3 yana yawon kashe dabbobi a yankunan. Malaman gandun daji sunyi nasarar kama shi a yayin da yake bacci a karkashin wata bishiya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG