Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Amanar Mata Da Maza Ke Yi Bai Sa Su Zama Mutanen Banza Ba - Inji Funke Adesiyan


Funke Adesiyan, yar wasan kwai kwayo ta Nollywood ta gaya wa matan Nigeria, cewar cin amanar da maza keyi bai zama cewa namiji mutumin banza bane sai dai ma ace ya sa shi ya zama rikakken namiji.

Yar wasan kwaikwayon tace mata su dunga mantawa da cin amanar da mazaje ke yi su maida hankali akan yanda mazajen ke kula dasu, ta kara da cewa tunanin ka rabu da miji saboda yana cin amana tamkar yin kaura ne daga Nijeriya zuwa Amurka, saboda ruwan sama.

Ta rubuta a shafinta na dandalin sadarwar Istagram, cewar rabuwa da namiji saboda cin amana kamar kayi kaura ne daga Nigeria, zuwa Amurka saboda ruwan sama, ki samu namijin kirki da zai soki ya mutunta ki, duk wani kalubale ya biyo bayan wannan. Maza an halicce su ne don suci amana saboda haka kar ki kalli gazawar sa, ki kalli yarda yake kula da ke.

Tace barkanku da kwana jama’a, na karanta sakonni da yawa akan rubutun da nayi, abun dariya mata na kare mazajen su akan basa cin amanarsu, yar uwata ki kyalesu su ansa da kansu, gaskiya daci gareta.

Ba zaka iya kare ma wani fada ba, Ina nan akan bakana dari bisa dari, na sani a matsayi na matar zamani muna kokarin mu bar wannan tsarin mu koma tsarin turawa amma ku yarda dani yana faruwa ko ina wadanda aka kama sune ake gani masu laifi, ba duka maza bane zasu fadi hakikanin gaskiya suce suna tare da matayensu shekara goma ba tare da cin amana ba, wannan bai maida su mutanen banza ba sai dai sunansu na Maza.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG