Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakarun Wasan Tennis Na Duniya Djokovic Da Nadal Sun Shiga Zagaye Na 3


Shahararren dan wasan ‘Tennis’ na biyu a duniya Novak Djokovic, ya samu nasarar shiga gasar zakaru ta duniya da za’a gwabza a kasar Madrid.

Dan wasan da ya lashe wasan koli a jere sau 12, y aba dan wasan kasar Spen Wildcard Nicolas kashi, yana kuma dakon zakara Feliciano Lopez.

Dan wasan mai shekaru 29, ya bayyanar da wannan nasarar da ya samu a matsayin abu mai wahala.

Dan wasan dai zuwa yanzu bashi da manaja, ya samu doke dan wasa Fabio Fognini, wanda shima ba kanwar lasa bane a wasan kwallon Tennis.

Haka shima dan wasan Birtaniya Andy Murray, ya kammala zagaye na uku a ranar Talata, da ya buge dan wasan kasar Romania Marius Copil.

Dan wasan Djokovic, yace yanasa ran daukar manaja kamin wasan kasar Faransa a ranar 28, ga wannan watan. Ya kara da cewar zuwa yanzu dai bai san wanda zai dauka ba.

Mutane dai nata raderadin cewar ga wanda zan dauka, don kawai nace inason wanda ya taba zama kamarni a fagen wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG