Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakiya "Janet Jackson" Ta Haihu Tana Da Shekaru 50 A Duniya!


Mawakiya Janet Jackson.
Mawakiya Janet Jackson.

Yawan shekaru ba tsufa ba! Shahararriyar mawakiya “Janet Jackson” da mijinta Wissam Al-Mana, sun karbi haihuwar sabon jariri. Ita dai mawakiyar, kanwa take ga shahararren mawakin duniya “Michel Jackson” Mawakiyar dai mai shekaru hamsin 50, a duniya ta haifi jariri da suka sama suna Elissa Al Mana.

Wannan haihuwar ta bama mutane da yawa mamaki, ganin cewar ta haihu tana da shekaru hamsin 50. Yanzu haka dai Janet, da jaririn suna cikin koshin lafiya. A shekarar da ta gabata ne, mawajiyar ta dakatar da wata tafiyar bude ido da ta shiryar a fadin duniya.

Dalilin ta kuwa shine don ta samu dama ta maida hankali ga juna biyu da take dauke da. Tun a shekarar 2012 Janet da Al Mana, suka yi aure. Amma sai a wannan shekarar suka samu haifu ta faro.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG