Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitattun Jaruman Bollywood 2016


A shekarar 2016, jaruman Bollywood, sun taka rawar gani a fegen fina finai, amma an fidda biyar daga cikinsu wadanda suka sami karbuwa, koda yake akwai mamaki ganin yadda wasu jaruman suka yiwa suran zarra.

Wadannan Jarumai biyar din da Bollywood, ta fitar a matsayin wadanda suka fi karbuwa ko kuma suka taka rawar gani da samun makudan kudade sune Akshay Kumar, Salman Khan, Aamir Khan, Shah Rukh Khan da Sushant Singh Rajput.

Akshay Kumar, shi ya kasance na daya, amma kada ya baku mamaki saboda ya cancanci ya kasance na daya domin ya jarjirce wajan aikin fitar da fina finai ukku masu suna Airlift, Housefull 3 da Rustom, inda ya nuna kwarewa da bajinta a wadannan fina finai.

Ya kasance abin sawa ido,domin shi bai yarda da yin fim din jeka nayika ba ya gwamace duk fina finansa su kasance abin bugun kirji.

Shi kuwa Salman Khan, a kowace shekara yana kasancewa a cikin fittatun jaruman Bollywood,biyar tunda fim dinsa na Sultan ya far samar masa kudi kamar hauka babu shaka ya ji a jikinsa kafi wannan fim din ya kammala koda yake kwaliya ta biya kudin sabulu.

Sai na ukku, Aamir Khan, wanda shi kuwa fim dinsa Dangal, ya baiwa masu kushe mamaki inda ya baiwa jama’a, abinda suke so suka kuma jinjinamasa akan wannan fim din kuma akwai yuwarfim din ya doke Sultan.

Shah Rukh Khan, wanda ya zo na hudu abin ya zo da mamaki ko da yake ba laifinsa bane daraktan fim din ne ya jawo fim dinsa na Zindagi rashin tabuka abin kirki.

Sai wanda ya zo na biyar Sushant Singh Rajput, wanda shi kuma Mahendra Singh Dhoni, ya baiwa fim din da ya bashi gurbi a Bollywood.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00

XS
SM
MD
LG