Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwa Mafi Yawan Shekaru A Fadin Duniya, Ta Cika Shekaru 177!


Tsohuwa Emma Morano
Tsohuwa Emma Morano

Emma Morano, itace tsohuwar da tafi tsawon rai a fadin duniya, tsohuwar mai shekaru dari da goma sha bakwai 117, tayi bukin cikar ta shekarun, da bayyanar da cewar tana da sauran karfin ta. Ta hure wutar kyandiran dake saman kek din da aka yimata lokacin bukin. Tsohuwar ‘yar asalin garin Verbania a kasar Italiya ce.

Shugaban kasar Italy, Mr. Sergio Mattarella, ya aika mata da katin murna, kuma ya bayyana a gidan talabijin na fadar shugaban, don taya ta murna da fatar Allah ya bata tsawon kwanaki da lafiya masu albarka.

An bata nau’in abinci da tafi sha’awa, a rayuwar ta da madara a yayin bukin. Lokacin bukin, ta gayama mutanen da suka halarci bukin cewar, ba dai zasu sata yanka kek din ba dai? sai ta kara da cewar, gaskiya naji dadi matuka da Allah ya nuna mun wannan ranar da na cika wadannan shekarun.

Awowi kadan bayan bukin sai ga wani kek, daga shugaban karamar hukumar garin da take. Ya kawo mata don karrama ta, inda yayi jawabin cewar, Morano, itace daya tilo da ta rage a cikin mutanen zamanin ta daga shekarun 1880.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG