Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Tsibirai Masu Hadari Ga Rayuwar Dan'adam A Fadin Duniya!


Tsibirin Limahuli Dake Kasar Hawaiian.
Tsibirin Limahuli Dake Kasar Hawaiian.

Bincike ya tabbatar da wasu tsibirai a fadin duniya, da suke da matukar hadari ga rayuwar dan’adam. Don haka aka hana mutane ziyartar wuraren. Tsibirin “Ramree Island” a kasar Burma, shine yanki da ake da manya-manyan dabbobin ruwa da ba’a cika samun su a koina ba a fadin duniya.

Haka tsibirin “Ilha Da Queimada” dake kasar Brazil, wanda akan yima kirari da tsibirin macizai, wannan shine tsibiri da macizai kanyi shawagi kamar yadda kwari ke kaiwa da kawowa. Bincike ya tabbatar da cewar tsibirin yafi kowane irin alkarya yawan macizai a fadin duniya.

Shi kuwa tsibirin “North Sentinel” mutane da ke rayuwa a wannan tsibirin sune mutanen da kawai suka rage a duniya, yanzu haka basu da wani alaka da abun zamani. Rayuwar su irin ta mutanen da, kuma basu da bukatar hada kansu da wasu jinsin mutane da ba irin suba.

Tsibirin “Farallon” shine tsibiri na farko da yake kasar Amurka, yana daga cikin tsibirai da mutane basu iya zama a yankin, saboda tsabar sanyi da gumaguman duwatsu da suke yankin. Gwamnatin kasar Amurka, ta gina wani dakin binciken da mutane kanje yanki daga lokaci zuwa lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG