Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jackie Chan Ya Samu Babbar Karramawar "Oscars Governors Awards"


Jackie Chan
Jackie Chan

Tun bayan assasa gidauniyar karrama jaruman fina-fina,i na kungiyar Hoolywood ta “Oscars Governors Awards” a ‘yan shekarun baya, akan zabi ‘yan wasa da suka taka muhimmiyar rawa, a wajen samar da fina finai masu kayatarwa, da samar da hotuna masu inganci, an karramar da mutane da dama.

Bisa al’adar wannan gidauniyar, sun karrama shahararren dan wasan fina-finai Jackie Chan, wanda ya lashe kyautar tare da wasu mutane uku, da suka hada da Mr. Anne V. Coates, shugaban tsare-tsare na finafinai da Ms. Lynn Stalmaster, ma rubuciya da bada umurni a fagen fina-finai.

Akan bada wannan karamawar ne a duk shekara, a dai-dai lokacin da ake zakulo wadanda suka taka rawar gani a shekarar da ta gabata, don kara musu karfin gwiwa. Ana wannan bukin don kara jaddada ma zakarun irin gwanintar su, hakan kuma na kara bama sauran mutane damar jajircewa don kokarin samun kyautar a shekara mai zuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG