Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Amurka Ta Sami 'Yar Najeriya Wadda Ta Hallaka Mijin Ta Da Laifi


Kotu a kasar Amurka ta kama ‘Yar Najeriyar mai zama kasar Amurka Temitope mai shekaru 36 da haihuwa da laifin kisan mijinta wanda ta yi ikirarin cewa maciyin amana ne kuma ya ci zarafinta, wata guda kafin ta soke shi da wuka har lahira.

Kotu ta tuhumi matashiyar da aikata laifin amfani da makami wajan aikata kisan kai inda lauyanta ya bayyana cewa ta aikata hakan ne cikin halin kunci da damuwa.

Mujallar News Journal ta jihar ta kasar Amurka ta wallafa cewa yanzu haka a maimakon ci gaba da sauraren karar da aka shirya yi a tsakiyar watan Oktoba da muke ciki, Temitope na fuskantar dauri kama daga shekaru hudu zuwa hamshin a gidan kaso.

A cikin watan afirilun shekarar 2015 ne Temitpe ta dabawa mijinta Adeyinka Adebayo wuka ne a gidan su dake Amurka, an kira jami’an ‘yan sanda da misalin karfe 12am na dare inda suka iske shi a sume da rauni kusa da wuyansa.

‘Yan sandan sun yi awon gaba da dukkan mutanen dake cikin gidan tare da Matar wadda take sanye da kaya duk jinni.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa Tomitope da mai gidan ta sun yi aure kusan sama da shekaru goma da suka gabata, kuma suna da ‘ya’ya biyu, matar ta bayyanawa jami’ai masu bincike cewar marigayin ya dade yana ci mata zarafi har a lokacin da take da juna biyu, kuma ya dade yana cin amanarta da wasu mata, harda ma ‘yar uwarta ta jini da kuma diyar mai reno ‘ya’yan su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG