Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Zasu Fitar Da Sabuwar Waya Sati Mai Zuwa!


Kamfanin Apple
Kamfanin Apple

A cikin sati mai zuwa ne idan Allah, ya kaimu shahararren kamfanin “Apple” zasu fitar da sabuwar wayar su, ta shekarar 2016. Ana sa ran kamfanin zai bayyanar da sabuwar wayar iPhone, a babban birnin San Francisco, a kasar Amurka.

Kamfanin sun gayyaci ‘yan jarida da sauran al’umma da su hallara a ranar Litinin 7, ga watan Satunba don bayyanar sabuwar wayar. Kamfanin dai basu bada wani cikakken bayani ba, irin yadda suka saba. Bisa ga al’ada dai sukan fitar da sababbin wayoyi guda biyu a kowace shekara.

Hakama ana sa ran kamfanin zasu bayyanar da wasu cigaba, da suka samar a agogon kamfanin da kwamfutar tafi da gidan ka. A cikin watanni 12 kamfanin dai sun siyar da sama da wayoyi milliyan dari biyu da sha hudu. Duk dai da cewar cinikayyar su yayi kasa a bana. Yanzu haka dai sun kayatar da sabuwar wayar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG