Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Inganta Harkokin Ilimi Zai Rage Fita Waje


Zainab Mustapha Matasa Ilimi
Zainab Mustapha Matasa Ilimi

A yau mun sami zantawa da wata Matashiya Zainab Mustapha Zakari, matashiya da ta je neman ilimin a kasar Cyprus da Masar inda ta ce dalibai na fuskanta kalubale mussamam ma daga yan kasa da ma malamai wanda baya rasa nasaba da wariyar launin fata.

Ta bukaci hukumomin Najeriya, dasu gaggauta inganta harkokin ilimi a Najeriya domin maido da maratabar ilimin jami'oin Najeriya, da kuma magance rajin aiki domin dalibai su sami kammala karatu akan lokaci.
Zainab, ta kara da cewa gine ginen jami'oin Najeriya da dama na bukatar suma a inganta su tana mai cewa muddin aka inganta harkon ilimin jami'oi na Najeriya tabbaci hakika za'a sami raguwar masu fita waje domin neman ilimin jami'a.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

XS
SM
MD
LG