Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karnuka Sunyi Yaga-Yaga Da Jaririya Mai Kwanaki 3 A Duniya!


Karnukan Da Suka Kashe Jaririya
Karnukan Da Suka Kashe Jaririya

Wata mazauniya jahar California, a kasar Amurka, Mrs. Macias, mai shekaru talatin da uku 33, ta hadu da masoyanta sun zama makiyanta na har abada. Bayan daukar juna biyu na tsawon watanin tara, ta haifi jaririya mace, kwanaki uku da haihuwar yarinyar.

Tana zaune a cikin gida da kanin ta, sai ta bar jaririyar a cikin daki da kofa sake, a cikin gidan su, suna zaune da wasu karnuka guda biyu 2, cikin rashin sani karnukan biyu sun shiga dakin da jaririyar take, kuma sun yima jaririyar munmunan rauni wanda kamin kaita asibiti ta mutu.

A cewar jami’an ‘yan sanda, lallai binciken su ya nuna cewar mahaifiyar ko wani, basu da sa hannu akan abun da ya faru da jaririyar, kawai karar kwana ne. Abun dai ya faru ne a matsayin zuwan lokaci. Yanzu haka dai an mika karnukan biyu hannun jami’an kula da dabbobi don duba lafiyar su da kuma daukar matakin da ya kamata da su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG