Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada - hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A fannin saye da sayarwa da zawarcin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, kungiyar Arsenal na zawarcin dan wasan kungiyar Santos Gabriel Barbosa, mai shekaru goma sha tara da haihuwa bayan sun rasa dan wasan Lacester City mai suna James Vardy.

Ita kuma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake ingila ta kammala sayen dan wasan Southampton mai suna Sadi Sadio Mane, mai shekaru 24 da haihuwa akan kudi fan miliyan talatin da hudu, wanda yafi kowane dan wasa tsada a gungiyar Liverpool. Hakan ta kasance ne bayan kungiyar ta sayi Carol, a shekarar 2011 daga kungiyar kwallon kafa na Newcastle.

Fitaccen dan wasa Mane ya daga riga a kungiyar Liverpool mai lamba goma sha tara (19).

Sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Spain, tana kan zawarcin dan wasan baya mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Hector Bellerin, domin maye gurbin dan wasanta Danny Welbeck, daya koma juvenyus buga wasa daga kungiyar Barcelona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG