Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ajiye Takalmin Lionel Messi Ya Bar Baya Da Kura


Gobe idan Allah ya kaimu za’a ci gaba da gasar nahiyar Turai, a matakin kwata painal tsakanin kasar Poland da Portugal, wanda ake bugawa a kasar Faransa.

Dan wasan kasar Portugal, wanda ake bugawa a kasar Faransa, dan wasan Portugal mai bugawa Fenerbahes, mai suna Nani, yace wasan da zasu buga gobe da kasar Poland, zai zama wasan da yafi kowane wasa burge masoyansu, yace wasan da suka buga a baya har sau hudu uku daga ciki sun yi kunnen doki ne.

Dan wasan Manchester United, wanda ke jagorancin kungiyar kwallon kafar kasar Ingila Rooney, yace ko kusa shi bashi da niyyar daina bugawa kasar Ingila kwallon kafa a yanzu, wanna ya biyo bayan rade radin dake fitowa kafafen watsa labarai cewa zai ajiye takalman sa saboda mai horar da ‘yan wasan kasar ta Ingila, ya ajiye aikin sa biyo baya kashin da suka sha a hannun Iceland.

Rooney, yace duk mai horar da ‘yan wasan da aka Kawo zasu tafi tare domin ciyar da kasar sa ta Ingila gaba.

Ajiye takalma da Lionel Messi, yayi ta bar baya da kura domin a yanzu haka Sergio Aguero, wanda yake bugawa kungiyar Manchester City da Javier Mascherano, mai bugawa kungiyar Barcelona, suma sunyi ikirarin ajiye takalman su, inda ake harsashen cewa watakila a samu wasu ma nan gaba da zasu ajiye takalmansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG