Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A bangaren hada hadar kasuwanci da zawarcin zaratan ‘yan wasan kwallon kafa, sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho na shirye shiryen sayen dan wasan Arsenal mai suna Aaron Ramsey mai shekaru 25 da haihuwa akan tsabar kudi fan miliyan 35.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kuma ta fara tattaunawa da kungiyar Real Madrid domin ganin yada zata yiwu dan wasan kungiyar Alvaro Morata mai shekaru 23 da haihuwa komawa kungiyar ta Chelsea.

Ita kuma kungiyar West Brom nada ra’ayi wajan sayen dan wasan Newcastle mai suna Andrew Sounset mai shekaru 24 da haihuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Intermilan dake kasar Italy na shirye shiryen sayen dan wasan kungiyar Man City mai shekaru 31 da haihuwa mai suna Pablo Zabaleta.

Shi kuwa mahaifin dan wasan nan Kelechi Ehinacho wanda ke buga wa kungiya Manchester City wasa cewa yayi babu inda Kelechi zai je a kakar bana, dan haka yana nan daram a kungiyar, mahiafin dan wasan ya bayyana haka ne a sakamakon wasu rade radi da suke fitowa cewar sabon mai horas da ‘yan wasan kungiyar Pep Guardiola na shirin bada aron dan wasan zuwa wata kungiya.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifin dan wasan ya bayyana hakanne a wata jarida mai suna Africanfootball.com inda y ace wannan bayani babu kamshin gaskiya a cikinsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG