Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Kona Shi A Dalilin Wayar Hannu


Wasu matasa a Calabar babbar birnin jihar Cross Rivers, sun nakadawa wani matashi kashi wanda daga bisani suka kona shi a gefen titi.

Shi dai wanna matashi mai suna Chidozie, ya gamu da ajalisa ne biyo bayan satar wayar hannu wato salula da yayi.

A binciken da jaridar Vanguard ta gudanar yayi nuni da cewa Chidozie, dai dan wata kungiyar fashi ne na mai mutane biyar, da suka addabi al’umar gari ko a ranar da aka kashe shi tare suke amma su sauran suka ranta a na kare shi kuwa akai yi rashin sa’a aka cim mashi.

Bincken ya kara da cewa a makon da ta gabata ne aka sako shi Chidodie, daga gidan yari kuma rahotanin na nuni da cewa shi dai Chidozie, ko makarantar sakadaren bai kammala ba domin a aji biyu na babban sakandare aka kore shi daga makaranta.

XS
SM
MD
LG