Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samson Siasia Yace Har Yanzu Babu Tabbas


Samson Siasia
Samson Siasia

Samson Siasia, babban Koch din kungiyar kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 23, wato Flying Eagles, na Najeriya, har yanzu yana ko kwanto ko Alex Iwobi na Arsenal da Kelechi Iheanacho na Manchester City zasu sami bugawa Najeriya wasa a gasar Olympics na 2016, da za’a yi a Brazil.

Siasia ya fadawa manema labarai a Abuja, cewa Arsenal, bata son baiwa Iwobi, damar zuwa ya bugawa Najeriya wasa saboda suna da bukatar yin amfani dashi a wasanin share fagge.

Koda yake yana sa ran cewa tana iya yuwa idan mahifin Iwobi,ya shawo kan Arsene Wenger, akan batun amincewa ya baiwa Iwobi damar ya takawa Najeriya leda a Olympic na bana.

Ita kuwa Manchester City, kawo yanzu bata bada amsa ba akan neman da aka yi na barishi ya takawa Najeriya, leda a wasani Olympics.

XS
SM
MD
LG