Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Cafke Wani Matashi Mai Tuka Keke Napep Akan Fashi Da Makami


Nigeria Fuel Shortage
Nigeria Fuel Shortage

Rundunar ‘yan sanda ta masamman akan yaki da ‘yan fashi da makami, ta cafke wani matashi matukin Keke Napep, mai suna Muyideen Ibrahim, da mukarabansa Ramonu Sanusi Rilwanu Ayinde Sodiq Olaide da Kazeem Idris wanda ake zargi da fashi da makami.

An cafke shine tare da wasu ‘yan fashin da ake zargi da aikatar fashi da makami a Lagos, dan shekaru 29, ya bayana wa ‘yan Sanda cewa wasu daga cikin makamai da ‘yan fashi ke amfani dashi ‘yan siyasa ne suka basu alokacin yakin neman zabe.

Ya kara da cewa ‘yan bangar siyasa da dama basu maida makaman da aka basu ba a lokacin yakin neman zabe, wanda dashi wasu ke fashi .

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Muyideen Ibrahim, yace yana amfani da Keken Napep, din shi wajen daukar makaman da ‘yan fashi ke aikata ta’asar su dashi, yawancin ‘yan bangar siyasar in ji Ibrahim, ‘yan kungiyar asiri ne.

Yace an kama shine a lokacin da aka zo kama wani Dagbe Ahmed, dan kungiyar asiri da yake zaune tare dashi wanda shi bai san cewa dan fashi bane a cewar sa.

Da yake tabbatar da labarin Kwamishinan ‘yan Sanda Fatai Owoseni, yace sauran ‘yan kungiyar ‘yan fashin da ake nema sun hada da Oshanleke da Sodiq Kashi

XS
SM
MD
LG