Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Da Su Kafi Kashe Kudi Wajen Yakin Duniya!


Kasar India, na daya daga cikin kasashe a duniya dake kashe makudan kudade don yaki a fadin duniya. A jerin kasashen da sukafi kashe kudi a wajen yaki ko dai don samar ma ‘yan kasar su tsaro ko taimaka ma wasu kasashen duniya samun tsaro. India itace kasa ta shida da suke kashe kimanin dallar Amurka billiyan $51.3B.

Kasar France, itace kasa ta bakwai a cikin jerin kasashen da suke kashe kimanin dallar Amurka billiyan $50.9B. Haka kasar Japan, tazo da takwas, inda suma aka kiyasta kudin da suke kashewa da suka kai dallar Amurka billiyan $40.9B.

Kasa ta tara kuwa a cikin jerin kasashen da su kafi kashe kudi a wajen yaki a duniya itace kasar Germany, haka suna kashe kimanin dallar Amurka billiyan $39.4B. Kasa kuwa ta goma itace kasar Koriya ta kudu, sukan kashe kudi da suka kai sama da dallar Amurka billiyan $36.4B.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG