Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsunto Kwarangwal Mai Shekaru 4,800 Na Uwa Da Jariri A Hannu!


A dai-dai lokacin da ake tunkarar ranar mahaifiya ta duniya, sai gashi jerin wasu masana arzikin karkashin kasa da sanin tarihi “Archaeologists” a kasar Taiwan, sun hako wani burbushin kasa da ke nuna kasusuwan jikin wata uwa tare da danta a rungume.

An dai kiyasta yawan shekarun wannan da suka kai kimanin shekaru dubu hudu da dari takwas 4,800. A iya tasu fahimtar sun iya gano cewar wannan uwar da jaririn ta, sun mutu ne a sanadiyar yunwa, wanda yanayin yadda uwar take kallon yaron na nuna yadda uwa take tsakanin ta da da ko a wancan zamanin.

Babban abun mamaki da yadda tsarin kasusuwan suke shine, yadda uwar take rike da jaririn a hannun ta, kuma tana kallon shi har suka mutu a tare fuskar ta, bata bar kallon jaririn ba. A cewar daya daga cikin masu binciken, a kasar ta Taiwan, suna amfani da wasu na’urori ne wajen gano yawan shekarun duk wasu kasusuwa da suka tsunta. Domin kuwa a ‘yan kwanakin baya sun gano wasu kasusuwan yara biyar da suma suka mutu shekaru da dama. Kasusuwan na kuma nuni da alamun suna iya zama halittar mutane na farko ne a doron kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG