Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Basu Jidadin Matakan Da Hukumar NFF Ta Dauka Ba


Nigeria Soccer Oliseh
Nigeria Soccer Oliseh

'Yan Kwamitin dabarun kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta Najeriya, sun ajiye aikin su.

Hakan ya biyo bayan rashin amincewarsu akan matakan da hukumar ta kwallon kafar Najeriya,ta dauka a bisa al’amari da ya shafi mai Horas da ‘yan wasan Najeriya Sunday Oliseh.

’Yan kwamitin da suka ajiye aikin nasu sun hada da Christain Chukwu, Paul Bassey, Victor Ikpeba, Mutiu Adepoju da Garba Lawal.

‘Yan Kwamitin sun nuna rashin jidadinsu dagane da matakan da shugaban hukumar ta kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick, ya dauka na rugawa wurin Ministan matasa da wasanni, bayan su ‘yan kwamitin sun tabbatar cewa Sunday Oliseh, ya saba ka’idojin kwantragin sa wanda yake nufin batun sallamar say a rage.

Shugaban kwamitin Barrister Chris Green, ya tabbatar da ajiye aikin nasu amma yace yana kokarin shawo kansu ko zasu canja shawara.

XS
SM
MD
LG