Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A Kasar Indiya Sun Kama Wata Akuya Da Laifi


Rahotanni daga kasar Indiya sun bayyana yadda wani jami’in dansandan kasar ya kama wata akuya da mai ita bisa aikata laifin banna da akuyar ta yi a wani lammbun babban ma’aikacin gwamnati.

A jiya litini ne ‘yan sandan jahar Chhattigash suka dauki mataki akan mutumin da akuyar sa a sakamakon kama ta da aka yi tana cin ganye a lambun gundumar majistare da ke yankin.

Koda shike rahotanni sun bayyana cewar an bada belin mutumin da akuyar sa, amma ana tuhumar su da laifin karya doka da bannata kaya, a cewar daya daga cikin jami’an mai suna Ram Sewak Paikra daga Janakpur a gundumar Korea.

Jami’in ya kara da cewa “da farko akuyar da mai ita na hannun jami’an ‘yan sanda amma yanzu an bada belin su kamar yadda kundin tsarin mulki kasar sashe na 427 da 447 ya tanadar. kodashike akuyar ta dade tana aikata wannan laifi a cikin garin Janakpur dake da kwatankwacin kilomita 340 arewa daga birnin Raipur".

An bada belin Abdul Hasan da akuyar tasa ne bayan ya furta cewar bazai sake barin akuyar ta aikata irin wannan mummunan laifi ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG