Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Real Madrid Marcelo Ya Goce a Kafada


A yau talata ne kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Real Madrid ta fitar da sanarwar cewa zata iya kasancewa dan wasanta na cikin gida Marcelo bazai sami halartar wasan zakarun turai da za'a buga a Roma sati mai zuwa ba a sakamakon gocewar kafada da yake fama da ita.

Marcelo mai shekaru 27 wanda ya zamo dan gaban goshin sabon kocin tawagar 'yan wasan Zidane, ya goce kafada ne ranar lahadi a yayin da kungiyar take fafatawa a wassanin La Liga da wasan ya tashi da ci 2-1 a birnin Grenada.

Kulob din ya ce an binciki lafiyar dan wasan, amma ba'a bada tabbacin rana ko lokacin da zai fara fita domin cigaba da taka leda ba, wanda ya danganta da lokacin da dan wasan ya sami sauki.

A cewar kafafen yada labarai na Spaniya, zai iya yiwuwa bazai yi wasa har na tsawon sati uku ba, hakan na nuna cewa bazai sami halartar wasan La Liga da kungiyar tasu zata buga da Athletic Bilbao ba da kuma wasan zakarun turai zagaye na biyu da kungiyar zata kara da kulob din Italiya a ranar 17 ga watan fabarairu ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG