Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Zasu Kasa Su Tsare, Su Kuma Raka


Matasa a fusace su na kona tayoyi da tarkace domin su nuna rashin yardarsu da janye tallafin farashin mai da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta yi, Lagos Talata, 10 Janairu 2012.
Matasa a fusace su na kona tayoyi da tarkace domin su nuna rashin yardarsu da janye tallafin farashin mai da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta yi, Lagos Talata, 10 Janairu 2012.

Wasu matasa a Najeriya sun lashi takobin cewa a bana dai, ba zasu bari 'yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da fritina domin kawai su ci gaba da zama kan karagar mulki, ko kuma su kwaci madafun ikon kasa ba.

Da yake tattaunawa da Dandalin VOA, wani shugaban matasa mai suna Comrade Yakubu Hashim Kabo, yace a bana, zasu tabbatar da cewa sun kasa sun tsare, sun kuma raka domin tabbatar da ganin an samu irin canjin da suek bukata.

Yace su na ci gaba da wayar da kan matasa domin gujewa zamowa 'yan barandan 'yan siyasa, tare da rungumar sana'a domin dogaro da kai.

Yace a wannan karon, zai yi matukar wuya 'yan siyasa su iya maida matasa karnukan farautarsu.

Matasa Sun Waye - 2'06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG