Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwarto Ya Addabi Mutanen Unguwar Kofar Ruwa Kashin Farko


Mutanen Unguwar Kofar Ruwa a Kano sun koka game da wani kwarton dake shiga cikin gidajensu idan sun fita sallar asuba, yana far ma matansu ta hanyar tsirata su da wuka.

Dandalin VOA ya tattauna da wasu mutanen unguwar wadanda suka ce wannan mutumin, ya jima sosai yana kai farmaki a gidajensu.

Wani magidanci mai suna Alhassan Aliyu Gobirawa, yace yau shekaru uku ke nan wannan mutumin yana tsallakawa cikin gidajen mutane. Yace shi kansa a shekarar da ta shige, wannan kwarto ko dan fyade ya shiga gidansa, inda Allah Ya taimaka aka gano shi tun kafin yayi barna.

Ga kashin farko na bayanin wannan kwarton.

Kwarto Ya Addabi Mutanen Kofar Ruwa A Kano Na Daya - 1'20"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:23 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG