Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mutum ya Rabu da Matarsa Sakamakon ta Haifi 'yan ukku


Wasu na murnar haihuwa wasu kuma ba sa so. labarin wani mutum ke nan da matarsa

Wata mace ta haifi ‘yan ukku amma kuma mai gidanta ya rabu da ita sakamakon hakan, babu kulawa daga ita har yaran da ta Haifa balle ma ya zo ya ganta. Hakan yasa matar kokawa da irin halin da take ciki.

A na sa bangaren kuma, mahaifin yaran ya amince da cikin, amma tun da farko ya nuna baya son cikin.

A lokacin da yayi hira da Baraka Bashir wakiliyar Dandalin muryar Amurka, mahaifin yaran yace bai taba hana matarsa abinci ba, amma tun da farko wasu mata ne suka fara gaya masa cewa matar da ya aura tana dauke juna biyu.

kamar yadda za ku ji a nan, ga cikakkiyar hirar da Dandalin VOA yayi da mahaifin yaran.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG