Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsige Aminu Maigari Daga Shugabancin Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya


Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, wanda majalisar zartaswar hukumar ta ce ta tsige shi a yau alhamis

Kwanaki kadan a bayan da ya tsallake rijiya da baya tare da taimakon FIFA, yanzu majalisar zartaswa ta Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta tsige shugaban hukumar, Alhaji Aminu Maigari, daga kan kujerarsa.

Yau alhamis aka tsige shi a lokacin da wakilai 8 suka jefa kuri'ar yin hakan, shi kuma ya samu goyon bayan wakilai guda 5 kawai.

Majalisar zartaswar ta hukumar NFF ta nada mataimakin shugaban hukumar na daya, Cif Mike Okeke Umeh, a zaman shugaban riko kafin a gudanar da sabon zabe a ranar 26 ga watan Agusta.

Wata sanarwar da aka bayar a karshen taron da majalisar zartaswar ta yi, ta ce, "a bayan da aka yi nazari tare da muhawara mai zurfi a kan yadda ake gudanar da harkokin kudi na hukumar nan cikin sirrin da bai kamat ba, tare da rashin kiran taron majalisar zartaswa na tsawon watanni 8, watau a cikin tsakiyar lokutan da aka yi ta daukar muhimman shawarwari kan harkar kwallon kafa a Najeriya, kuma 'yan mutane kalilan a cikin majalisar suka dauki shawarwarin, mun zartas da kuri'ar rashin amincewa da shugabancin Alhaji Aminu Maigari."

XS
SM
MD
LG