Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an SSS Sun Kama Aminu Maigari


Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Alhaji Aminu Maigari

Labarai da dumi-duminsu na cewa jami’an tsaron SSS a Najeriya sun kama shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, suka tafi da shi.

Yau jumma’a da safe jami’an tsaron suka kama Alhaji Aminu maigari da wasu membobin hukumar kwallon kafa ta Najeriya a lokacin da jirginsu ya sauka a Abuja daga kasar Brazil.

Jiya alhamis aka ce an rushe majalisar gudanarwar hukumar kwallon kafar ta Najeriya bisa umurnin wata kotu da ta ce su daina daukar kansu a zaman masu gudanar da harkokin kwallon kafa na Najeriya.

Tsohon shugaban Firimiya Lig na Najeriya, Rumson Baribote, shi ne ya shigar da karar a babbar kotun Jos yana neman a hana Aminu maigari da dukkan kwamitoci da majalisun hukumar kwallon kafar Najeriya gudanar da duk wata harkar da ta shafi kwallon kafa a kasar.

XS
SM
MD
LG