Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Masu Shirin Kai Hari Yau Alhamis Kan Filin Jirgin Saman Entebbe


Wani bangaren bataliya ta 3 ta sojojin Uganda a filin jirgin saman Entebbe, lokacin da suke shirin tashi zuwa aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliya.
Wani bangaren bataliya ta 3 ta sojojin Uganda a filin jirgin saman Entebbe, lokacin da suke shirin tashi zuwa aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliya.

Ofishin jakadancin Amurka dake Uganda yayi gargadi game da yiwuwar wani harin ta'addanci a kan babban filin jirgin saman Entebbe a kasar Uganda.

Ofishin ya fada a shafinsa na Intanet cewa majiyoyin leken asiri sun ce akwai wata "takamammiyar barazanar" da aka samu daga wata kungiyar ta'addanci cewa zata kai hari kan filin jirgin saman yau alhamis 3 Yuli tsakanin karfe 9 zuwa karfe 11 na dare.

Ofishin yace ya samu bayanin wannan barazana ce daga rundunar 'yan sandan Uganda.

Ofishin ya bukaci matafiya da zasu bi ta wannan filin jirgi da su sake nazarin shirinsu, su kuma yi hattara.

XS
SM
MD
LG