Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Ja Kunnen Najeriya, Ta Ba Ta Wa'adin Nan Da Talata


Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, tana iya dakatar da Najeriya daga duk wata harkar kwallon kafa, a bayan da aka cire shugabannin hukumar kwallon kafar kasar, aka kuma tsare shugabanta Aminu maigari, a lokacin da suka koma Najeriya daga gasar cin kofin duniya a Brazil.

Jiya jumma’a, hukumar FIFA ta ja kunnen gwamnatin Najeriya da cewa tilas ta maida ‘yan kwamitin zartaswar hukumar kwallon kafar Najeriya kan kujerunsu nan da ranar talata, ko kuma a haramta ma kasar shiga duk wata harkar kwallon kafa.

Hukumar ta fada cikin wata sanarwa cewa, “FIFA ta samu labarin tsare shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Aminu Maigari, wanda jami’an hukumar SSS suka yi.” Wannan ya biyo bayan doke Najeriya da kasar Faransa ta yi da ci 2-0 ran litinin a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya.

A shekarar 2010 ma, gwamnatin Najeriya ta dauki irin wannan matakin a lokacin da aka yi waje-rod da Super Eagles na Najeriya a gasar cin kofin duniya. A lokacin, shugaba Goodluck Jonathan ya yi barazanar soke kungiyar kwallon kafar kasar na tsawon shekara biyu, har sai bayan da hukumar FIFA ta sanya baki.

Dokokin FIFA su na kare dukkan hukumomin kwallon kafa 209 na kasashen dake cikinta daga tsangwamar gwamnatocin kasashensu, kuma irin dakatarwar da FIFA keyi tana haramtawa dukkan kungiyoyin kwallon kafa na kasa tare da jami’ansu shiga duk wani wasa ko wani taro da wata kasar.

XS
SM
MD
LG