Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tunkuda Keyar Kasar Kamaru Zuwa Gida


kwallo a cikin ragar kasar Kamaru a gasar cin kofin duniya
kwallo a cikin ragar kasar Kamaru a gasar cin kofin duniya
To fa an tunkuda keyar kasar Kamaru a gasar cin Kofin Duniya inda ta sha kashi da ciya-ciyayy 4-0.

Wato abunda ya samu Kamaru kamar targade ne ya jawo karaya, saboda har jirginsu ya nufi hanyar gida bayan jan kunne da Croatia tayi mata.

Idan ba’a manta ba, Kamaru taje har wasannin kusa da karshe a kofin duniyar 1990, kuma ita ce kasar farko a Afirka da ta samu damar zuwa wannan rukuni, amma a jiya dai Croatia tafisu yawan ‘yan wasa, da kuma yin wasa mai kyau, saboda haka yanzu babu yadda za’a yi Kamaru taje zagaye na biyu a wannan gasa.

Wato Eto’o wanda shine mafi kwarewa a kungiyar yaji rauni a gwiwarshi ta dama, amma abubuwa basu dagule wa kungiyar ba, sai bayan da Alex Song yabi wani dan wasan Croatia yayi masa gula, kuwa nan take aka bashi jan kati.

Karshen tonon asiri kuma shine fada da ‘yan kungiyar suka fara yi tsakaninsu, wato Benoit Ekotto ya kaiwa Benjamin Moukanjo farmaki. Lallai akwai tambayoyi da yawa akan kungiyar Kamaru gaskiya.
XS
SM
MD
LG