Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tuhumi Matashin Da Yayi Yunkurin Hallaka Dantakarar Shugabancin Amurka Donald Trump


Jiya Laraba ne aka tuhumi wani matashi dan kasar Britaniya kan zargin mallakar makamai, bayan da jami'an tsaro suka ce yayi yunkurin kashe dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump a farkon watan nan, a wani gangami a birnin Las Vegas.

Masu taya masu gabatar kara gaban kotu tabbatar da tuhuma da ake kira Garand Jury da turanci, sun tuhumi Michael Sanford dan shekaru 20 da haihuwa da zarge zarge biyu, na daya cewa shi yana Amurka ba bisa ka'ida ba, na biyu kuma ya mallaki makami, da hanawa ko kuma kassara tafiyarda harkokin gwamnati.

Ana iya yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan fursina, amma ba'a tuhume shi da kisa makarkashiyar aikata kisan kai ba.

Sanford wanda yayi tattaki daga California zuwa Las Vegas, ya kuma yi kokarin zare bindigar wani dansanda dake samar da tsaro a wajen gangamin na siyasa, yace yaje ne da zummar kashe Donald Trump, kuma idan bai sami nasara ba a Las Vegas, yana da wani shiri na sake kokarin aikata haka a Jihar Arizona.
Akwai rahotannin Sanford bashi da koshin lafiya ta wasu fuskoki.

Donald Trump
Donald Trump

Trump Attempted Attack
Trump Attempted Attack

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG