Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Ado Daukaka Mako Guda Bayan Sace Shi


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa SP Usman Abubakar ya mika fitaccen mawakin nan na jihar Adamawa Ado Daukaka wanda ya share mako guda a hannun wadanda suka sace shi a ranar juma’ar data gabata biyo bayan wata waka mai taken gyara kayanka da ya raira inda ya caccaki wasu ‘yan siyasar jihar.

Kakakin ‘jami’an ‘yan sandan ya mika mawakin ga iyalai da kuma ‘yan uwa a shalkwatar ‘yan sandan jihar ta Adamawa bayan wadanda suka sace shi sun jefar dashi a wani wuri dake bangaren Lafiya Lamurde dake jihar ta Adamawa.

Jami’in ya kara da cewa an samo mawakin ne daure, amma daga nan aka garzaya dashi zuwa asibiti inda aka bashi magunguna da kulawa dai dai gwargwado, sa’annan aka kaishi shalkwatar ‘yan sandan jihar domin mika shi ga iyalansa.

A ranar juma’ar data gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi awongaba da mawakin biyo bayan wata waka da ya raira akan cin hanci da rashawa a jihar Adamawa, lamarin da yasa wasu ‘yan siyasa da dama suka bata rai.

Da suka tattauna da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz ta wayar tarho, Ado ya bayyana masa cewa zai iya tunawa da farko ‘yan bindigar sun fara aje shi ne a yankin Wuro jabbe, inda ya kwashe kwanaki biyu a hannun su, daga nan kuma suka kara gaba da shi zuwa hanyar Numan amma bazai iya tabbatar da inda suka yada zango ba.

Mawakin ya kara da cewa daya daga cikin ‘yan bindigar ya yi masa tambayar cewar mai yasa shishshiginsa ya fara wuce gona da iri? Ya kuma kara da cewa idan ya motsa a lokacin zai fasa masa kwakwalwa da bindiga.

Daga karshe Ado Daukaka ya bayyana cewa shidai yasan wakar da yayi wadda ya fallasa halayen wasu ‘yan siyasa ce kadai yake zargin ta tunzura wasu har suka kaiga yi masa haka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG