Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Egypt Ke Kawowa Ghana Cikas A Faggen Kwallon Kafa


Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana Kwesi Nyantakyi ya furta cewa Ghana zata fuskanci kalubale da Egypt awsan da zasu na shiga gasar cin kofin kwallo kafa ta duniya ta shekarar 2018.

Ghana da Egypt zasu fafata da juna a cikin rukunin E tare da kasashen Congo da Uganda a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Ghana ta lallasa Egypt ne a karawarsu na shiga gasar da akayi a Brazil. Shugaban na hukumar kwallon kafa na Ghana, yana kyautata zaton Egypt ce zata zamawa Ghana kalubale a cikin rukunin E.

Yace wannan rukuni ne mai wahalar gaske, yace Uganda da Congo duk masu kokari ne amma dai Egypt ce ta dade tana kawowa Ghana cikas.

Kwesi Nyantakyi yace “na kalli wasu wasannin sun samu sabbin yan wasa kuma kungiyarsu tayi kyau “Amma yace Ghana, zata yi kokarin lashe duk wasanin ta kuma ya kyautata zato cewa zasu samu nasarar shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.

XS
SM
MD
LG