Zaratan Gasar Kasashen Turai Za Su Fara Taka Leda A Yau

A yau Talata 17 ga watan Satumbar 2019, za'a fara gasar cin kofin zakarun Turai (UEFA Champions League) a matakin rukuni.

Kungiyoyi 32 da suka fito daga lig-lig na kasashen turai daban-daban zasu fafata a matakin wasa rukuni, bisa tsarin rukuni guda 8.

Wasannin da za'a fara sune kamar haka, Borussia Dortmund da ta karbi bakoncin Barcelona, sai kuma Inter Milan da Slavia Prague a rukunin F, kana Napoli zata kara da Liverpool, sai Salzburg da KRC Genk a rukunin E.

A rukunin G, Lyon na kasar Faransa da Zenit St Petersburg, akwai wasan Benfica da RB Leipzig.

A sauran wasan kuwa a rukunin H, akwai wasan Ajax da Lille, Chelsea na kasar Ingila, zata karbi bakoncin Valencia ta kasar Spain.

Wasannin za'a fara tun daga misalin karfe shida saura minti biyar na yammaci, da kuma wadda za'a fafata takwas na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Ghana.