Wani Dan Kasuwa Ya Shiga Hannun Hukuma

Wata kotu a Igbsere, jihar Legas, ranar Laraba ta yanke wa wani dan kasuwa mai shekaru 47 da haihuwa Maduabuci Onwuta, hukuncin daurin gidan yari har na shekaru 25 a sakamakon fyade da ya yi wa yarinya ‘yar watani 16 da haihuwa.

Mai shari’a Sedotan Ogunsanya, yayin da take gabatar da hukuncin, ta ce mai gabatar da kara ya yi bayani babu kokwanto akan wannan laifi.

Ta ce “na samu wanda ake zargi da laifin yi wa ‘yar yariyar fyade, kuma na yanke masa hukuncin daurin zama kurkuku har na tsawon shekaru 25, hukuncin zai fara aiki nan take daga ranar da aka yanke shi”.

A lokacin da ake sauraron karar, mai gabatar da karar ya bayyana cewa Mr Adebayo Haroun Maduabuci, ya aikata wannan laifi a ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2013, a yankin Isheri.

Laifin fyade ya sabawa dokar laiffufuka ta Jihar Legas sashe na 137, wanda ya bukaci hukuncin kisa ko daurin rai da rai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin.