Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ki Bada Belin Maryan Sanda


Babbar kotun kasa dake birnin Abuja ta ki amincewa da takardar belin Maryam Sanda da aka gabatar a gaban kotu, wacce ake zargin ta da kashe mijin ta, Bilyamin Bello.

An gurfanar da Maryam, ‘yar Maimuna Aliyu, wacce ta gudanar da bankin Aso Savings a da, inda ake zargin Maryam da kisan mijin ta dan tsohon shugaban jamiyar PDP Mohammed Bello.

Lauya Joseph Dauda, SAN, mai wakiltar Maryam ya roki kotu da ta yi mata afuwa domin neman kula daga asibiti, ganin tana dauke da juna biyu.

Alkali mai sauraron karar ya kori takadar belin a rananr Laraba saboda rashin ingancin takardar.

Halilu ya ce, sanarwar rokon ta sabawa hukuncin da kotu ta yanke kwanakin baya, inda aka ki amincewa Maryam beli, a ranar 14 ga watan Disamba.

Ya kara da cewa abinda ya kamata ace anyi shine a gabatar da takardar kudirin dakatar da karar, amma rashin yin hakan ya sa aka bukaci sake gabatar da ita a ranar 25 ga watan 1 na shekarar 2018.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG