Tauraron Kamfanin Wayar Hannu OnePlus Ya Haskaka

A karon farko kamfanin wayoyin zamani na kasar China OnePlus yayi cinikin dala Biliyan guda, kuma ya samu riba, wadda ba kasafai akan samu wannan nasara ba a kasuwar wayoyin zamani mai cike da gasa.

Shugaban kamfanin OnePlus Pete Lau, ya ce a shekarar da ta gabata kamfanin yayi cikinikin sama da dala Biliyan 1.4 wanda ya zo da riba mai tsoka.

Wannan ci gaba dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da OnePlus ya shirya kalubalantar manyan kamfanonin fasaha ta hanyar sayar da wayoyinsa a Amurka da Turai.

A ‘yan shekarun nan kasuwar wayoyin zamani ta cika da gasa a China, inda samun riba ya zama wani abu mai wuya, wanda hakan ya jefa manyan kafanoni da suka yi fice irin su HTC da Motorola faduwa.

Birtaniya ta zamanto babbar kasuwa a Turai, inda OnePlus ya samar da ma’aikata 30 a ofishinsa na London. Mr. Lau ya ce kamfanin na shirin ci gaba da fitar da sabbin wayoyi biyu a duk shekara, kuma zai kaddamar da sabuwar wayar ta OnePlus 6 cikin wannan shekarar.

Your browser doesn’t support HTML5

Tauraron Kamfanin Wayar Hannu OnePlus Ya Haskaka