Super Falcons Za Ta Sake Karawa Da Black Queens A Gasar WAFU

Kungiyar kwallon kafar mata ta Super Falcons za ta sake karawa da kungiyar hamayya ta kwallon kafar mata ta Black Queens a gasar cin kofin mata na WAFU.

Manyan kungiyoyin wasan kwallon kafar ta mata da ke Afirka, wato Super Falcons ta Najeriya da Black Queens ta kasar Ghana za su fafata a yau, yayin da suka hadu a wasan kusa da na karshe a gasar WAFU a Cote d'Ivoire.

Idan har kungiyar ta Falcons, ta yi galaba akan kungiyar Black Queens, hakan tamkar ramuwar gayya ce, domin ‘yan wasan na Ghana sun lallasa 'yan wasan Najeriya kafin su kai matakin karshe.

Dukkan kungiyoyin sun kauce wa haduwa da juna a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta mata, wacce Ghana ta karbi bakoncinsa a bara, yayin da Ghana ta ke jaograntar rukunin A, su kuma Super Falcons dake rukunin B na jagorantar rukunin.