Sunannakin Gwarazan Kwallon Kafa Na Duniya Su Shida

Jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa shida da za suyi takara, wanda za'a zaba a matsayin gwarzo dan wasan kungiyar firimiya lig na bana a kasar Ingila.

Cikin 'yan wasan akwai 'yan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City guda uku a cikinsu da aka bayyana don zaben gwarzon, wanda suka hada da Bernardo Silva da Raheem Sterling da kuma Sergio Aguero.

Ita kuwa Liverpool tana dauke da 'yan kwallo biyu da suka hada da Virgil Van Dijk, da kuma Sadio Mane, sai kuma dan wasan Chelsea, Eden Hazard, shi ne cikon na shida, a cikin sune za'a zabi wanda za'a karrama a matsayin gwanin bana na PFA.

Mohammed Salah na Liverpool ne ya lashe kyautar a shekarar da ta wuce 2017 zuwa 2018. A bangaren zaben matashin 'yan wasa na bana kuwa a akwai 'yan wasan Ingila uku da ke takarar gwarzon matashin dan wasa na kungiyar na bana da suka hada da Marcus Rashford na Manchester United mai shekara 21 da haihuwa da Trent Aledander-Arnold mai shekara 21 na Liverpool.

Na ukun shi ne dan wasa baya na kungiyar kwallon kafa ta West Ham United, Declan Rice, mai shekaru 20 a duniya akwai kuma dan wasan Bournemouth mai shekara 21, David Brooks.

A shekarar da ta gabata dai Sterling ne ya zama matashin da yafi taka rawa a kungiyar ta PFA, inda ya lashe kyautar a shekarar 2018.

Bisa tsari dai, sai dan wasa mai shekara kasa da 23 ne kuma wanda ke buga wasa na gasar firimiya shi ne zai cancanci shiga gasar, matashin da yafi kwazo a kungiyar kwararrun 'yan wasan firimiya za su zuba.

Ranar 28 ga watan Afirilu bana ne za'a bayyana sunayen zakarun da suka samu nasara a London Grosbenor House.